Shugaban Karamar Hukumar Igabi, Honarabul Sani Abdul Kamfanin Zangon Aya, ya jaddada kudirinsa na tallafa wa harkokin jin kai da walwalar al’umma, bayan da ya halarci taron kaddamar da IGABI LAFIYA WAQAF FOUNDATION tare da bude Asusun Tallafi (Appeal Fund), wanda aka gudanar a Cibiyar National Teachers Institute (NTI), Kaduna.
Taron, wanda ya samu halartar manyan baki daga sassa daban-daban na jihar Kaduna, ya kasance wani muhimmin mataki na hadin gwiwa tsakanin gwamnati da kungiyoyin jin kai domin tallafa wa marayu, marasa galihu da kuma gajiyayyu a cikin al’umma. A yayin taron, an bayyana manufofi da tsare-tsaren da IGABI LAFIYA WAQAF FOUNDATION ta sanya a gaba domin inganta rayuwar al’umma, musamman a bangaren lafiya da jin kai.
Da yake jawabi a wajen taron, Hon. Sani Abdul Kamfanin Zangon Aya ya bayyana jin dadinsa da kafa wannan gidauniya, yana mai cewa irin wadannan kungiyoyi su ne ginshikin cigaban al’umma, musamman a lokacin da ake fuskantar kalubalen tattalin arziki da zamantakewa. Ya kara da cewa, gwamnati ba za ta iya yin komai ita kadai ba, don haka hadin gwiwa da kungiyoyin jin kai na da matukar muhimmanci.
A matsayin goyon baya ga wannan aiki na alheri, Shugaban Karamar Hukumar Igabi ya bayar da gudunmuwar kudi har Naira miliyan biyu (₦2,000,000.00) domin tallafa wa ayyukan gidauniyar. Wannan gudunmuwa ta samu yabawa daga mahalarta taron, inda suka bayyana ta a matsayin abin koyi ga sauran shugabanni da masu hannu da shuni.
Ba wannan kadai ba, Hon. Sani Abdul Kamfanin Zangon Aya ya kuma bayyana cewa tun kafin gudanar da wannan taro, ya riga ya bayar da tallafin Naira miliyan daya da dubu dari biyu (₦1,200,000.00) ga IGABI LAFIYA WAQAF FOUNDATION, domin taimakawa shirye-shiryen kaddamar da gidauniyar da kuma nasarar gudanar da taron. Wannan ya nuna tsayuwarsa tsayin daka wajen ganin ayyukan jin kai sun samu nasara.
Shugabannin gidauniyar sun bayyana godiyarsu ga Shugaban Karamar Hukumar Igabi bisa wannan gagarumin tallafi, inda suka ce gudunmuwar za ta taimaka matuka wajen cimma burikan gidauniyar, musamman a bangaren tallafawa marayu, marasa galihu da marasa lafiya.
A karshe, mahalarta taron sun yi addu’a ga Hon. Sani Abdul Kamfanin Zangon Aya, suna rokon Allah Madaukakin Sarki Ya saka masa da alheri, Ya sanya wannan gudunmuwa ta zama masa ladan alheri a mizani, tare da albarkaci rayuwarsa da aikinsa na shugabanci. Haka kuma, an yi addu’a ga mambobin IGABI LAFIYA WAQAF FOUNDATION da duk masu tallafa wa ayyukan jin kai, Allah Ya saka musu da alheri mai yawa, Ya kuma kara musu ikon ci gaba da taimakon al’umma baki daya.
