Hukumar Jin Daɗin Alhazan Jihar Kaduna ta fara mayar wa kowane mahajjaci Riyal 123 na Saudiyya a matsayin kuɗin da suka rage sakamakon bambancin canjin kuɗi da aka samu yayin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026.
Shugaban Hukumar, Malam Salihu Sani Abubakar, ne ya bayyana hakan yayin wani taron musamman da aka gudanar da alhazan jihar a masaukinsu da ke Ibrahim Khalil a birnin Makkah bayan sallar Azahar ranar Litinin.
A cewarsa, Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta ƙayyade canjin kuɗi na Dala 500 da ake bai wa kowane mahajjaci a matsayin Basic Travelling Allowance (BTA) da Naira 1,443 kan kowace Dala ɗaya. Wannan ya sa jimillar kuɗin da aka ware wa kowane mahajjaci ta kai Naira 721,500.
Malam Salihu ya bayyana cewa kafin a fara jigilar alhazai zuwa ƙasar Saudiyya, darajar Naira ta samu ƙarin ƙarfi a kasuwar canjin kuɗi, lamarin da ya sa farashin Dala ya ragu zuwa Naira 1,350 da Kobo 74. Wannan sauyi ya rage kuɗin da ake buƙata wajen samar da Dala 500 ga kowane mahajjaci zuwa Naira 675,370.
Ya ce sakamakon wannan canjin ya haifar da ragowar kuɗi da ya kai Naira 46,130 ga kowane mahajjaci, wanda ya zama wajibi a mayar masa domin tabbatar da gaskiya da adalci wajen gudanar da harkokin Hajji.
Shugaban hukumar ya ƙara da cewa bayan nazari da tuntuba, an samu canjin Riyal na Saudiyya da farashin Naira 375 kan kowace Riyal, wanda ya bai wa hukumar damar sauya ragowar kuɗin zuwa Riyal 123 na Saudiyya ga kowane mahajjaci. Ya bayyana cewa bayan wannan lissafi, har yanzu akwai ragowar Naira 5 da ke kan asusun kowane mahajjaci.
Malam Salihu ya ce an fara rabon kuɗaɗen ne bayan sallar La’asar ta ranar Litinin, inda aka fara da alhazan da suka isa ƙasar Saudiyya a jirgin farko. Ya bayyana cewa an tsara yadda za a ci gaba da rabon ga sauran alhazai domin tabbatar da cewa kowa ya karɓi haƙƙinsa cikin sauƙi da tsari.
Ya kuma tabbatar wa alhazan cewa duk wanda yake son karɓar ragowar Naira 5 ɗinsa zai samu damar yin hakan bayan dawowarsa Najeriya, domin tabbatar da cewa babu ko sisi guda da za ta ɓace daga kuɗaɗen da suka rage.
Shugaban hukumar ya jaddada cewa manufar hukumar ita ce gudanar da harkokin Hajji cikin gaskiya, riƙon amana da bin ƙa’idojin da suka dace. Ya ce hukumar za ta ci gaba da tabbatar da cewa duk wani kuɗi da ya shafi alhazai ana tafiyar da shi cikin tsari mai kyau da cikakken bayani.
A wani bangare kuma, alhazan jihar Kaduna sun yaba da wannan mataki da Hukumar Jin Daɗin Alhazan Jihar Kaduna ta ɗauka, suna masu bayyana shi a matsayin wata alama ta gaskiya, riƙon amana da kyakkyawan shugabanci.
Mahajjatan sun kuma jinjinawa Kwamitin Musamman na Hajji ƙarƙashin jagorancin Malam Salihu Sani Abubakar saboda yadda ya tafiyar da harkokin Hajjin bana cikin buɗaɗɗen tsari da rikon amana. Sun bayyana cewa mayar da kuɗaɗen da suka rage ba tare da wata matsala ba ya nuna irin ƙoƙarin da hukumar ke yi wajen kare haƙƙin alhazai da kuma tabbatar da cewa an gudanar da dukkan harkokin kuɗi yadda ya kamata.
Wasu daga cikin alhazan da suka halarci taron sun bayyana farin cikinsu da wannan ci gaba, suna masu cewa irin wannan tsari zai ƙara wa jama'a kwarin gwiwa da amincewa da yadda ake gudanar da harkokin Hajji a jihar Kaduna.
Sun yi addu’ar Allah Ya saka wa shugabannin hukumar da alheri, Ya ba su ikon ci gaba da gudanar da ayyukansu cikin gaskiya da nasara, tare da fatan cewa za a ci gaba da inganta walwala da jin daɗin alhazan jihar a shekaru masu zuwa.
